Ana ci gaba da kai kayan agaji a Siriya
September 22, 2016Babban jami'in asibitin al-Quds Dr. Hamza al-Khatib ya tabbatar da mutuwar mutane 45 a wani harin bama bamai ta sama da aka kai a sansanin 'yan tawaye da ke birnin Aleppo. A farkon wannan makon madai anzargi jiragen yakin na dukkanin bangarorin da je jagorantar yaki a Siriya da kai hari kan motocin dakon kayan agaji dake wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 20 ciki har da wani jami'in agaji na Red Cross.
To sai dai jami'in Majalisar Dinkin Duniya a Siriya RAMZY Ezzeldin akwai kyakkyawar fatan sake zaman sulhun dan kawo zaman lafiya nan gaba, to amma shugaban kasar Siriyan Bashar al-Assad na ganin hannu da sauran manyan kasashen duniya ke da shi a rura wutar rikici ke hana cimma tsagaita wuta a kasar.
"A shirye muke da ko wace irin tattaunawa da zai tabbatar da zaman lafiya a Siriya, to amma kasashen Amirka da sauran kasashen kamar saudiya da ke maramata baya basa da niyar ganin ankawo karshen murza wuta a Siriya."