Zaben Amirka ya dauki hankalin duniya
November 4, 2020
A kasar Amirka ana ci gaba da kirga domin tantance mutumin da zai lashe zaben shugaban kasa tsakanin Shugaba Donald Trump na jam'iyyar Republican da babban mai adawa da shi Joe Biden na jam'iyyar Demokrat.
Kalilan na jihohi suka rage amma su ne za su tantance gwani tsakanin 'yan manyan 'yan takaran wadanda kowanne yake yunkurin kai wa ga gaci, na samun yawan kuri'un wakilan masu zaben shugaban kasa. Duk dan takara da ya samu yawan wakilan da ke zaman shugaban kasa 270 shi ne zai zama shugaban kasa na gaba, kuma dan takara zai iya samu idan ya lashe galibin wakilan da aka raba tsakanin duk jihohin kasar 50.
An samun tsaikon saboda yadda ake ci gaba da kirga milyoyin kuri'u na mutanen da suka yi zabe ta hanyar aikewa da wasiku, sakamakon annobar cutar coronavirus, kawo yanzu akwai jihohi kusan 10 da suka rage.