1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da mawuyacin hali a Yankin Gabas ta Tsakiya

March 24, 2011

Mai yiwuwa ƙasar Iran ta bunƙasa ma'adaninta na Uranium sakamakon hare-haren da ƙasashen yammaci ke kai wa Libiya

https://p.dw.com/p/10h4x
Masu zanga-zangar adawa da gwamnati a ƙasar YemenHoto: AP

Masana harkokin ƙasa da ƙasa sun bayyana hare haren da Amirka da Faransa da kuma Birtaniya ke jagoranta akan Libiya, a matsayin wani dalilin da Iran za ta dogara akan sa wajen ci gaba da bunƙasa sinadarin niukiliyar ta, wanda ƙasashen yammacin duniya ke ganin domin ƙoƙarin ƙera makaman ƙare dangi ne, ko da shi ke kuma ita Iran ta sha nanata cewar na samar da makamashi ne.

A cewar Mark Fitzpatrick, ƙwararre a sha'anin yaɗuwar makaman ƙare dangi na cibiyar nazarin dabarun shugabanci na ƙasa da ƙasa, matakin da ƙasashen yammacin duniyar suka ɗauka zai ƙarfafa rashin yardan Iran da Amirka, kasancewar shugaban addinin ƙasar Iran Ayatollah Ali Khamnei ya furta cewar, da dai Libiya ba ta yi watsi da shirin uranium nata a shekara ta 2003 ba, to da kuwa ƙasashen basu yi tunanin farmata a yanzu ba.

Wannan bayanin yana zuwa ne a dai dai lokacin da ƙasar Faransa dake sahun farko wajen ƙaddamar da farmaki akan Libiya ta sanar da yin nasarar tarwatsa wani jirgin yaƙin gwamnatin LIbiya a birnin Misurata jim kaɗan bayan saukar sa a wani sansanin sojin saman ƙasar, ta hanyar wani makami mai linzamin da sojojin Faransar suka jefa daga jirgin sama.

Shi kuwa shugaba Mua'mmar Gaddhafi na LIbiya jaddada ƙira ya yiwa 'yan ƙasar da su tashi tsaye domin kare ƙasar su:

"Tilas ne ku shiga a dama da ku cikin wannan yaƙin. Wajibi ne ga 'yan ƙasa su shiga cikin wannan yaƙin. Ku yi ta gudanar da zanga-zangar nuna ƙyamar mamaya a ko ina cikin duniya, domin za ta taimaka muku wajen samun galaba. Ku gudanar da zanga-zanga a Afirka da Asiya da kuma Amirka baki ɗaya."

Zaman ɗarɗar a Benghazi

Libyen Krieg Gaddafi NATO Benghasi
Masu adawa da gwamnatin Gaddafi a Benghazi na maraba da hare-haren ƙasashen ƙawance na yammaciHoto: AP

A can Benghazi na Libiya, wanda ke hannun 'yan tawaye kuwa, mazauna birnin na ci gaba da zaman ɗar-ɗar game da yiwuwar dakarun dake goyon bayan shugaba Gaddhafi za su iya kai musu hari, inda galibin shaguna da wuraren kasuwanci ke ci gaba da kasancewa a rufe, abinda yasa shugaban Amirka Barak Obama ya ce har yanzu da sauran aiki a gaba:

"Muddin bai sauka daga muƙamin sa ba, to, Libiyawa za su ci gaba da fuskantar barazana. Mu kuma za mu ci gaba da bayar da gudummowar mu ga ƙoƙarin bada kariya ga al'ummar Libiya."

Siriya ta fara fuskantar bore

Syrien Daraa Proteste Demonstration
'Yan adawa da gwamnati a Daraa ta ƙasar SiriyaHoto: AP

Baya ga Libiya, ita ma ƙasar Syria tana fama da rikici tare da 'yan adawa, inda adadin mutanen da suka mutu sakamakon wani harin da gwamnatin ƙasar ta ƙaddamar akan wani masallacin da ta ce maɓoyar 'yan adawar ne ya ƙaru zuwa mutane 37. Sai dai kuma mai baiwa shugaban ƙasar Basshar al-Assad shawara akan harkokin labaru Buthaina Sha'aban ta shaidawa wani taron manema labarai ɗazun nan cewar gwamnatin tana ɗaukar matakan tabbatar da tsaro ga illahirin 'yan ƙasar, kana tana yin nazarin bitar dokar ta ɓacin da take yin amfani da ita tun cikin shekara ta 1963, wadda ta haramta yin kowane nau'i na bore.

A Yemen kuwa arangama ce dakarun dake biyayya ga shugaba Ali Abdallah Saleh suka yi tare da sojojin da suka yiwa gwamnatin sa bore, inda mutane ukku suka jikkata, yayin da tuni wasu ƙasashen yammacin duniya kuwa suka fara janye jami'an diflomasiyyar su daga ƙasar.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Ahmad Tijani Lawal