1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Babu yuwuwar tsagaita wuta tsakanin Armeniya da Azerbaijan

October 1, 2020

Ana ci gaba da artabu tsakanin kasashen Armeniya da Azerbaijan wadanda suka sun lashi takobi fadada rikicin da ke faruwa tsakanin bangarorin biyu.

https://p.dw.com/p/3jFl9
Armenien - Aserbaidschan Ein armenischer Soldat feuert auf aserbaidschanische Streitkräfte
Hoto: Hakob Margaryan/Photolure/Reuters

Kasashen Armeniya da Azerbaijan sun lashi takobin ci gaba da yakar juna dangane da rikicin da suke yi kan wanda ya kamata ya mallaki yankin nan na Nagorny Karabakh. A yayin da aka shiga rana ta hudu ana tashin hankali, kasashen sun sanar a ranar Laraba cewa babu sassauci sai kowa ya ga abin da ya turewa buzu nadi.

Jama'an da ke zaune a kusa da inda kasashen ke musayar wuta, sun bayar da labarin ganin fashe-fashe da sauran nau'ika na tashin hankali. Wannan kartar kasar da suke yi na zuwa ne a yayin da kasashen Rasha da Faransa ke kira a gare su da su tsagaita wuta a yi musu sulhu ta hanyar diflomasiyya. Kawo yanzu mutune 100 rikicin ya halaka cikin kwanaki hudu.