1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru biyu bayan sojoji sun kwace mulkin Mali

Suleiman Babayo LMJ
August 16, 2022

Shekaru biyu bayan sojoji sun kwace madafun ikon kasar Mali har yanzu kungiyoyin tsageru masu dauke da makamai na kawo tashe-tashen hankula.

https://p.dw.com/p/4FbYM
Soldaten in Mali
Hoto: Florent Vergnes/AFP/Getty Images

Kimanin shekaru biyu bayan sojoji sun kwace madafun ikon kasra Mali da ke yankin yammacin Afirka, har yanzu ana ci gaba da samun hare-hare kungiyoyin masu nasaba da jihadi.

A watan Agustan shekara ta 2020 sojoji suka kwace madafun iko daga hannun Marigayi Ibrahim Boubacar Keita saboda matsalolin da suka yi katutu ga kasar.

Tun farko sojojin sun kafa gwamnati karkashin farar hula kafin daga bisani Kanar Assimi Goita ya nada kansa a matsayin shugaban gwamnatin wucin gadi, inda haka ya haifar da takun saka da kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS, saboda batun tsara jadawalin mayar da kasar bisa tafarkin dimukaradiyya.