Ana ci gaba da yin tir da kutsen sojin Rasha a Ukraine
March 2, 2014Su ma kasashen duniya na yi ta kira ga hukumokin birnin Mosko da su girmama 'yancin yankunan kasar ta Yukren suna masu cewa matakin da Rasha ta dauka na girke dakarunta a yankin Krimea ya saba da dokokin kasa da kasa.
Bayan da majalisar dokokin Rasha ta amince da tura karin sojojin kasar zuwa yankin Krimea, shugaban hukumar tsaron Yukren Andrij Parubij ya nunar a wannan Lahadi cewa an umarci ma'aikatar tsaro da ta kira dukkan sojojin kasar. Tun kuwa a ranar Juma'a gwamnatin wucin gadin Yukren ta sanya sojojinta cikin shirin yaki. Yanzu haka dai sojojin Rasha sun mamaye kusan ilahirin yankin tsibirin Krimea, abin da Firaministan rikon kwaryar Yukren Arseniy Yatsenyuk ya ce kasarsa na dab da fadawa cikin wani bala'i.
Kutsen Rasha a Krimea wani bala'i ne
"Muna dab da shiga wani bala'i. Tarayyar Rasha ba ta da wani hurumin mamaye kasar Yukren. Mun yi imani abokanmu na kasashen yamma da gamaiyar kasashen duniya gaba daya za su mara wa kasarmu a matsayinta na 'yantacciya kuma hadaddiyar kasar Yukren."
Shi ma shugaban rikon kwarya Alexander Turtschinov wanda ya bayyana matakin Rasha na tura dakarunta da cewa tsokana, ya yi kira ga gamaiyar kasa da kasa ta dauki mataki na zahiri amma ba fatar baka ba kadai ba.
"Kasashen da ke ikirarin cewa su kawayen Yukren to lokaci ya yi da za su sauke nauyin da ke kansu. Dole su tallafa wa Yukren, dole kuma duniya ta dauki mataki na zahiri don dakatar duk wani kokari na yi wa kasarmu kutsen soji. Ina magana ne game da yankin Krimea inda sojojin Rasha suka mamaye wuraren da sansonin sojin suke."
Kira da a soke taron G8 a Sochi
Tuni dai kasashen duniya suka yi tir da matakin da Rashan ta dauka kana sun yi kira gareta da ta janye dakarunta daga yankin kasar ta Yukren ko kuma a dauki matakin jan kunnenta. Kasashen Faransa da Birtaniya tuni sun yi kira da a dakatar da shirin gudanar da taron kungiyar G8 da za a yi a yankin shakatawar nan na Sochi. Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya yi karin haske.
"Da farko mun yi tir da matakin sojin Rasha. Muna son a shiga tattaunawa ba da bata lokaci ba, ko dai kai tsaye tsakanin Rasha da Yukren wanda zai zama maslaha mafi kyau, ko kuma ta shiga tsakanin Majalisar Dinin Duniya da kungiyar tsaro da hadi kai ta Turai. Na biyu matakin Rashar ya saba da ka'idojin G7 da G8, saboda haka matsayin Faransa shi ne a dakatar da shirye-shiryen taron G8."
Mista Fabius ya ce kasarsa na mara wa Yukren a matsayin kasa mai cikakken 'yanci kuma za su tallafa wa sabbin hukumomin kasar musamman a fannin tattalin arziki.
A kuma halin da ake ciki babban sakataren kungiyar Nato Anders Fogh Rasmussen a wannan Lahadi ya kira taron gaggawa na dukkan jakadun kasashe 28 na Nato a kan rikicin na Yukren. A ranar Litinin kuma ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar EU za su gana don duba matakin da za su dauka game da kutsen sojojin Rasha a Yukren.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Pinado abdu-Waba