1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci-gaba da zanga-zangar ƙyamar shugaba Musharraf na Pakistan

September 24, 2007
https://p.dw.com/p/BuAS

A kasar Pakistan zanga-zangar nuna adawa da aniyar shugaba Pervez Musharraf na yin tazarce na kara bazuwa zuwa yankuna da dama na kasar. A birnin Islamabad daruruwan magoya baya wani kawance jam´iyun Islama sun yi macin nuna kyamar shugaba Musharaff wanda ke son a tabbatar da sabon wa´adin shugabancinsi na shekaru biyar a ranar 6 ga watan oktoba ba tare da ya ajiye mukamin sa hafsan hasoshin sojin kasar ba. ´Yan sanda sun kame mutane da dama musamman wadanda suka yi ta jifa da duwatsu a wajen kotun kolin kasar lokacin da kotun ta fara zaman sauraron kararrakin nuna adawa da wannan shiri na shugaba Musharraf. ´Yan sanda dauke da makamai da kulake sun toshe hanyar zuwa kotun.