1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daukar matan tsaro sakamakon sace wasu 'yan mata a Lagos

Kamaluddeen SaniMarch 3, 2016

Mai magana da yawun gwamnan jihar lagos da ke a Najeriya Habib Aruna ya bayyana cewar hukumomin jihar sun bayar da umarni ga jami'an tsaro dasu kara daukar matakan tsaro a makarantun jihar.

https://p.dw.com/p/1I6JA
Nigeria Gauck auf Staatsbesuch
Hoto: picture alliance/dpa/W. Kumm

Matakin dai na zuwa ne bayan da wasu 'yan bibdiga dadi sun kai farmaki tare da yin awan gaba da wasu 'yan mata uku da ke a cikin jihar.

Tun dai a ranar litin din nan ce 'yan bindiga dadin suka isa makarantar Babington Macaulay da ke a Ikorodu a jihar lagos tare da kwase 'yan makarantar, a inda wata majiya daga jihar tayi nuni da cewar 'yan bindigar sun nemi abasu kudin fansa daya tasarma naira miliyan 200 kwatankwacin dala miliyan daya, koda yake dai jami'an yansanda sun yi gum basu ce uffan ba.

Kazalika sanarwar ta ce gwamnan Akinwunmi Ambode na jihar bai ji dadi abin da ya faru ba, a don haka ya zama wajibi ayi farautar wadanda suka aikata danyen aikin.