Rikicin gwamnati a Jamus
July 2, 2018Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta shirya tsaf don kaddamar da wani shirin da zai janyo ra'ayin ministan cikin gida kuma shugaban jam'iyyar CSU, Horst Seehofer, jim kadan bayan ya sanar da aniyarsa ta sauka daga mukaminsa sakamkon kin amincewarta a kan bijoro da tsauraran matakai na dakile kwararar 'yan gudun hijira a kan iyakokin Jamus.
Shugabannin jam'iyyar CDU ta Angela Merkel da kuma na jam'iyyar CSU wadda Seehofer ke jagoranta za su gana a wannan Litinin a birnin Berlin, don nemo mafita a kan kwararar da baki ke cigaba da yi kasar ta Jamus.
Shi dai Seehofer na son a dauki tsauraran matakai da suka hada da komawa da 'yan gudun hijirar zuwa kasashen Turai da aka rigaya aka yi musu rajista ta masu neman mafaka. Amma Angela Merkel ba ta goyon bayan wannan shawara. Ta fi son a samu matsaya daya tsakanin kasashen kungiyar tarayyar Turai.