Ana cikin mawuyacin hali a asibitin Zirin Gaza
November 13, 2023Fada tsakanin dakarun Isra'ila da mayakan kungiyar Hamas a wajen asibitin nan na Al Shifah ya tilasta dubban mutane tserewa daga yankin, yayin kuma da wasu bayanan ke nuna cewa akwai daruruwan mutane da ke makale a ciki.
Ana dai ci gaba da nuna damuwa da halin da aka shiga a asibitin, daidai lokacin da likitoci ke cewa babu abinci da ruwan sha gami da wutar lantarki.
Baya ga daruruwan marasa lafiya da ke kwance a asibitin, akwai ma sauran fararen hula da ke fakewa a ciki.
Marasa lafiya ciki har da jarirai da dama ne ke mutuwa saboda halin da aka shiga.
Isra'ila ta ce cibiyoyin lafiya a yankin na kan shelkwatar kungiyar Hamas da aka gina a karkashin kasa.
Hare-hare 4,300 ne Isra'ila ta kaddamar a kan Zirin Gaza a yakin ramuwar gayya da ya biyo harin ba-zata na Hamas wanda ya kashe sama da mutum dubu da 400 a Isra'ila a ranar bakwai ga watan jiya.
Kungiyar Hamas dai kungiya ce da Tarayyar Turai da Amurka da Jamus da ma wasu kasashen duniya ke dauka a matsayin kungiyar ta'addanci.