1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana daf da samun allurar rigakafin Malaria

Mouhamadou Awal Balarabe
April 23, 2021

Jami'ar Oxford ta Birtaniya ta yi nisa a gwajin allurar rigakafin zazzabin cizon sauro da take yi, inda sakamako ya nuna ingancin kashi 77% a kasashe hudu na nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/3sVIp
Mücke, Blut saugend
Hoto: picture-alliance/dpa/P. Pleul

Wani gwajin allurar rigakafin zazzabin cizon sauro ya nuna ingancin da ba a taba ganin kwatankwacinsa ba a nahiyar Afirka, lamarin da ya haifar da fatan samun gagarumar nasara a yaki da cutar da ke yawan kashe yara kanana. Jami'ar Oxford ta Birtaniya da ta samar da wannan allurar rigakafin mai suna R21 / Matrix-M ce ta yi wannan shailar, inda ta ce ce a karon farko an cimma nasarar fiye da kashi 75% na ingancinsa kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tsara.
 
Babu dai wata illa da aka lura da ita yayin gwajin a kasashen Afirka hudu, kuma za a samar da rigakafin a farashi mai rahusa. Wannan rigakafin da Oxford ta yi aiki tare da Novavax na Amirka wajen samar da shi, za'a iya amincewa da shi cikin shekaru biyu masu zuwa.

kashi 94% na wadanda ke kamuwa da Malaria da wadanda take halakawa na da zama ne a nahiyar Afirka, kuma galibinsu yara ne, a cewar WHO.