Ana fama da takun saƙa tsakanin Kenya da Al-Shabab
October 30, 2011Daga cikin muhimman batutuwan da suka shiga kannun rahotannin jaridun Jamus dangane da al'amuran Afirka a wannan makon har da tashintashinar da ake fama da ita tsakanin Somaliya da Kenya, faɗan da aka ce a halin yanzu ya ɗauki wani sabon fasali, inda bisa ga dukkan alamu wasu ƙasashen yammaci suka tsoma hannunsu a ciki. A lokacin da take rawaito wannan rahoto jaridar Berliner Zeitung cewa tayi:
"A fafutukar murƙushe ƙungiyar Al-Shabab mai zazzafar aƙidar Islama a Somaliya, ƙasar na fuskantar hare-hare daga kusurwowi daban-daban. A ƙarshen makon da ya wuce wani jirgin ruwan yaƙin Faransa yayi ruwan bamabamai akan garin Kismao mai tashar jiragen ruwa a kudancin Somaliya, kamar yadda bayanai suka nunar. A baya ga haka ma dai jiragen saman yaƙin Faransar sun kai farmaki kan sansanonin ƙungiyar Al-Shabab a cewar majiyoyi masu nasaba da sojan ƙasar Kenya. Ita kanta Kenyar na shirin kai farmaki kan garin Afmadow dake hannun Al-Shabab a kudancin Somaliya. Dangane da haka farar hula suka fara tserewa daga garin."
Ita ma jaridar Süddeutsche Zeitung ta duba halin da ake ciki, inda ta ce a halin yanzu haka ƙasashen gabacin Afirka guda uku ne ke fafatawa a Somaliya. A baya ga sojojin Uganda da Burundi dake kare gwamnatin riƙon ƙwarya ta Sheikh Sharif Ahmad a Mogadishu, ita kuma Kenya a yanzu ta tura sojojinta zuwa kudancin Somaliya sakamakon sace wasu baƙi mata su huɗu da 'yan ta kifen Somaliya suka yi daga harabar ƙasarta. To sai dai kuma wanda ya san yadda al'amura zasu kaya nan gaba da kuma irin goyan bayan da Kenyar zata samu daga ƙasashen yammaci, saboda kawo yanzu kwamitin sulhu na MƊD bai ce uffan game da lamarin ba."
A Afirka ta kudu an kakkaɓe babban kwamishinan 'yan sanda da wasu ministoci guda biyu daga kan mukamansu sakamakon samunsu da laifuka na rashin gaskiya. Ɗaya daga cikin ministocin ma dai yayi amfani ne da baitul-malin gwamnati don kai wa budurwarsa ziyara a wani gidan yari dake Switzerland, a cewar jaridar Die Tageszeitung, wadda tayi nuni da cewar babban dalilin ɗaukar wannan mataki shi ne domin zama darasi ga sauran jami'an gwamnati, musamman ganin yadda gwamnatin ke fama da tofin Allah tsine da kuma cewar nan da watanni goma sha huɗu masu zuwa ne za a gudanar da sabon zaɓen shugaban ƙasa a Afirka ta Kudun.
A yayinda ƙasashen Turai ke fama da raguwar yawan al'uma, nahiyar Afirka sai bunƙasa take yi ba ƙaƙƙautawa, wannan shi ne kanun wani rahoton da jaridar Neue Züricher Zeitung ta rubuta dangane da bunƙasar yawan al'uma zuwa miliyan dubu bakwai a doron ƙasa. Jaridar ta ce ko da yake Afirka duka-duka kashi goma sha biyar cikin ɗari dake da shi na yawan al'umar duniyar nan tamu, a yayinda Asiya ke da kashi sittin cikin ɗari, amma a inda take ƙasa tana dabo shi ne kasancewar nan da wasu 'yan shekaru masu zuwa yawan al'umar zai riɓanya sau biyu, musamman ganin bunƙasar da nahiyar ta Afirka ke samu na kashi biyu da ɗigo uku a duk shekara.
Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal
Edita: Zanab Mohammed Ahmad