1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana iya zartas da kuduri kan Iran nan ba da dadewa ba

May 4, 2006
https://p.dw.com/p/Buze

Bisa ga dukkan alamu nan ba da dadewa ba, kwamitin sulhu na MDD zai zartas da wani kuduri wanda zai tilastawa Iran ta dakatar da shirin na inganta sinadarin Uranium. Ko da yake kasashen Rasha da China sun nuna adawa da wani sabon daftarin da kasashen Faransa da Birtaniya da kuma Amirka suka gabatarwa kwamitin sulhu. To amma Rasha ta nuna alamar amincewa da daftarin idan aka yi masa ´yar kwaskwarima. A cikin daftarin kudurin kasashen 3 sun bayyana shirin nukiliyar Iran da cewa babbar barazana ce ga zaman lafiyar duniya. A lokacin day ake tofa albarkacin bakinsa akan wannan batu shugaban kwamitin dake kula harkokin ketare na majalisar dokokin Jamus, Ruprecht Polenz, wanda ya kai wata ziyarar yini biyu a birnin Teheran, ya ce dole ne Amirka ta nuna shirin yin tattaunawa.