1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana Jiran sakamakon zaben shugaban Togo

Usman Shehu UsmanApril 26, 2015

Jama'a ba su fito da yawa ba a zaben shugaban kasar Togo da aka yi jiya, inda alamu suka nuna cewa shugaba mai ci yanzu zai samu damar yin tazarce

https://p.dw.com/p/1Ey9o
Togo Präsidentschaftswahlen
Hoto: I. Sanogo/AFP/Getty Images

A kasar Togo zaben ya gudana jiya Asabar kana bai samu fitowar jama'a ba. 'Yar mitsitsiyar kasar Togo da ke yammacin Afirka, na karkashin shugabancin iyali guda cikin shekaru aru-aru, inda a yanzu ma shugaba mai ci Faure Gnassingbé, ya nemi tazarce karo na uku.

Daga cikin wadanda ke kalubalantarsa a bangaren adawa sun hada da Jean-Pierre Fabre, wanda ya zo na biyu a zaben da ya gabata. Gnassingbé ya na rike da mulkin kasar to shekaru 10 da suka gabata, bayan da ya gaji mahaifinsa, wanda ya rasu kan mulkin kasar shekaru 38. Da fari dai an jinkirta zaben, bisa matsalar jerin sunayen masu kada kuri'a