Ana kokarin sasanta Rasha da Ukraine
November 26, 2018Talla
Manyan jami'an kasashen Jamus da Rasha da Ukarine da kuma Faransa na ganawa a birnin Berlin domin nazarin sabon rikicin nan da ya taso tsakanin Rasha da Ukraine.
Kasar Rasha dai na bijire wa kiraye-kirayen da kasashen duniya ke yi mata, na ta saki wasu jiragen ruwa mallakin kasar Ukraine.
Wasu jami'an Rashar ne dai suka harbi jiragen Ukraine a kan iyaka tare da kame wasu kusa da Crimea a karshen mako.
Ganawar a cewar kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamus, za ta maida hankali ne kacokan a kan rigimar ta karshen mako, don ganin yadda za a iya kaiwa ga samun maslaha.