1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana macin nuna adawa da gwamnatin Pakistan

August 14, 2014

Zanga-zanga ita ce mafi girma ta nuna adawa da cin hanci da ake samu a gwamnatin kasar Pakistan tun lokacin da Nawaz Sharif ya dauki madafun iko.

https://p.dw.com/p/1Cuub
Hoto: Reuters

Dubban mutane da ke gangamin nuna adawa da gwamnatin kasar Pakistan sun fara maci daga garin Lahore na gabashi zuwa Islamabad babban birnin kasar, abin da ya jefa tsoron yiwuwar samun tashin hankalin siyasa.

Ana gudanar da gangamin karkashin kungiyoyi biyu, da suka hada da wadda tsohon dan wasan cricket da ya zama dan siyasa Imran Khan yake jagoranta da kuma ta wani malamin Islama dan gwagwarmaya Tahir al-Qadri, inda suke nuna adawa da yadda cin hanci da rashawa suka yi wa gwamnatin kasar katutu. Tun farko gwamnati ta haramta gangamin, amma daga bisani ta mika wuya. Gwamnan Punjab Chaudhry Sarwar ya ce an bayar da damar saboda yadda mutanen suka amince cewa komai zai gudana cikin tsanaki.

Masu macin sun dade suna adawa da Firaminsitan kasar ta Pakistan Nawaz Sharif, wanda jam'iyyarsa ta lashe zaben da ya gabata.

Mawallafi: Suleiman babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal