Ana nuna damuwa ga yadda ake zubar da matattun kaji a Kano
February 4, 2007Talla
Yadda ake zubar da kajin da suka mutu sakamakon cutar murar tsuntsaye na sanya fargaba a tsakanin mazauna birnin Kano dake arewacin Nijeriya. Wani babban jami´i a jihar ya fadawa kamfanin dillancin labarun AFP cewa ba´a bin hanyoyin da suka dace wajen zubar da matattun kajin. Jami´in ya bayyana haka ne bayan da a jiya asabar kungiyar lafiya ta duniya WHO ta tabbatar da cewa cutar murar tsuntsaye ce ta yi sanadiyar mutuwar wata ´yar Nijeriya mai shekaru 22, wadda ta rasu cikin watzan janeru a birnin Legas. Matar dai ita ce ta farko da nau´in cutar H5N1 ya halaka a Nijeriya. Malam Shehu Bawa shugaban kwamitin jihar Kano dake yaki da murar tsuntsaye ya fadawa kamfanin AFP cewa sun samu rahoto daga garin Minjibir cewa wasu mutane da ba´a gane su ba sun zubar da matattun kaji kimanin 250 a wani juji.