Martanin huldar Baharain da Isra'ila
September 12, 2020Talla
Hamas ta kira Baharan da maciya amanar yankin Faladsinawa, tuni Faladsinu ta janye jakadarta a Baharain. Turkiyya ta yi barazanar katse huldarta da Baharain, amma Masar ta yi maraba da yarjejeniyar hulda tsakanin Isra'ila da Baharain.
Firaiministan Isra'ila Benjamin Natanyahu na fatan yarjejeniyar za ta samar da zaman lafiya da huldar kasuwanci. Tun dai bayan kafa Isra'ila 1948, Baharain ce ta zama kasar Larabawa ta hudu a Gabas ta tsakiya da ta sake shiga kawance da Isra'ila baya ga Masar da Jordan da kuma hadaddiyar daular Larabawa da ta cimma yarjejeniyar a baya-bayannan.