Ana zaben shugaban kasa a Faransa
April 10, 2022Wannan dai shi ne zaben shugaban kasa na 12 da ke gudana a karkashin jamhuriya ta biyar a Faransa, kuma karo na 11 ta hanyar kada kuri'a kai tsaye. Shugaba mai barin gado Emmanuel Macron, wanda ya lashe zaben shugaban kasa a 2017, na fuskantar adawa mai zafi, musamman daga mai tsattsaurar ra'ayin nan wato Marine Le Pen.
Sai dai masu nazarin alamura na cewa zaben na iya ba da wahalar samun dace na hasashe, kasancewar batun rikicin Ukraine cikin batutuwa na yakin neman zabe da ma yanayin fitar jama'a domin kada kuri'u a yau din.
Tuni dai wasu faransawa mazauna ketare suka yi nasu zaben a jiya Asabar, domin dacewa da bambancin lokaci, musamman kasashen da ke yankin tsibirin kudancin Pacific
Wasu masu hasashen dai na cewa akwai alamu Shugaba Macron ya iya zarta babbar abokiyar adwarsa Marine Le Pen da dan karamin rinjaye da zai iya kai su ga zuwa zabe zagaye na biyu a ranar 24 ga wannan watana Afrilu.