1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zargin jami'an Burundi da cin zarafi

March 9, 2017

Akalla kungiyoyin kare hakkin bil Adama 20 sun yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta sanya takunkumi kan wasu jami'an kasar Burundi bisa zargin take hakkin 'yan kasar.

https://p.dw.com/p/2YvOk
Burundi Soldaten
Hoto: picture alliance/dpa/W.Swanson

Kungiyar Human Right Watch na cikin gamayyar kungiyoyi da ke bukatar a ladabtar da wasu jami'an leken asirin Burundi da kuma wasu soji da 'yan sanda bisa laifukan cin zarafin fararen hula da ke kai ga kisa.

Akalla 'yan Burundi 5,000 ne ke gudun hijira a wasu kasashe makwabta, tun bayan barkewar rikicin siyasa sakamakon da shugaba Pierre Nkurunziza ya nemi zarcewa da karfin iko karo na uku a shekara ta 2015.

A baya-bayannan ma dai mashawarci na musamman a Majalisar Dinkin Duniya kan takaita kisan gilla Adama Dieng, ya gargadi cewar kasar Burundi ka iya fadawa cikin yakin basasa mafi girma matukar ba dauki matakan gaggawa kan cin zarafin al'umma ba.