SiyasaAfirka
Sojojin Burkina Faso sun kashe fararen hula
April 25, 2024Talla
Ana zargin sojojin kasar Burkina Faso da halaka kauyawa 223 ciki har da yara 56, a wasu kauyuka da ke yankin arewacin kasar sakamakon wasu hare-hare guda biyu. Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Right Watch a cikin wani rahoto da ta sake a wannan Alhamis ta ce sojojin sun kashe fararen hula da ake zargi suna hada kai da tsageru masu ikirarin jihadi, yayin da ake fuskantar tashe-tashen hankula tun shekara ta 2015.
Kungiyar ta ce ta yi hira da shaidun gani da ido da wadanda suka tsira daga wannan bala'i da ya faru a shekara ta 2022.
Ita dai Burkina faso da ke yankin yammacin Afirka tana cikin kasashen yankin Sahel da ake samun tashe-tashen hankula na tsageru masu kaifin kishin addinin Islama.