Andre Poggenburg na AFD ya yi marabus
March 8, 2018Talla
Andre Poggenburg dan shekaru 42 zai ajiye matsayinsa na shugaban 'yan majalisun na jam'iyyar AFD a Jihar Saxony Anhalt a karshen watan Maris. Ya ce zai yi marabus din ne domin samun sauki ga irin matsin lambar da yake samu daga kafofin yadda labarai tun bayan da ya yi tabargarzar, jam'iyyarsa ta AFD ta soki lamirin furcin nasa, kafin ta bukaci ya yi marabus.