Angela Merkel: Shekaru 15 a matsayin shugabar gwamnati
Tun a 2005 Angela Merkel ta hau mulki. Ga wasu daga cikin muhimman lokutan mulkin ta mai dogon zamani da ya kawo gagarumin sauyi a kasar baki daya.
"Yar gaban goshin Helmut Kohl"
Tsohon shugaban gwamnati Helmut Kohl da wasu manyan 'yan siyasa kan kirata "yarinya". Sai dai wannan matsayi ya sauya bayan ta zama shugabar jam'iyyar CDU mai adawa a 2001. Amma taurarinta sun fara haskakawa ne a 2005.
Nasara mai wahala
Zabukan kasa a 2005: Da kalilan kuri'u jam'iyyar CDU da CSU sun doke SPD ta shugaban gwamnati na wancan lokaci Gerhard Schröder. Hakika shi ne mafi munin zaben CDU a tarihinta, kuma somin tabi ga Merkel. Sai dai nan take mulkinta ya fara yin tasiri.
Sabuwar shugabar gwamnati
Jam'iyyun CDU da SPD sun yi hadakar kafa gagarumar gwamnatin hadin kan da zata mulki wannan kasa. Schröder ya taya Merkel murna, mace ta farko kana 'yar yankin gabashin Jamus kuma masaniyar kimiyya ta farko da ta zama shugabar gwamnati kazalika mafi karancin shekaru.
Mai masaukin bakin manya
Nan take Merkel ta nuna bajinta. A taron G8 a 2007, ta karbi bakuncin shugabannin kasashe takwas masu karfin tattalin arziki a birnin Heiligendamm da ke kan tekun Baltic. Tana cikin raha tare da shugaban Amurka na lokacin George W. Bush da Vladimir Putin na Rasha.
Halin samartaka
Barazana a siyasar Turai a 2008: Dole Merkel ta yi aiki kafada da kafada da manyan maza masu ji da kai, watau Shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa da fraministan Italiya Silvio Berlusconi. Kara durkushewar tattalin arzikin Turai ya zame babban damuwa ga kungiyar tarayyar Turai.
Taimako ko cikas?
Basussukan da ake bin wasu kasashen Turai ya kara habaka, wanda ke barazana ga Euro a matsayin kudi na bai daya. Tayin bada taimako a bangaren Merkel, ya zo da bukatun tsuke bakin aljihu. Hakan bai yi wa kasa kamar Girka dadi ba, inda jaridu suka rika wallafa hotunan kwatanta yanayin da mamayen 'yan Nazin Jamus a lokacin yakin duniya na biyu.
Mai yakin neman zabe da salo irin nata
A zahiri dai Merkel ba mai baiwar magana ba ce. Jawabanta na yawan tokarewa, babu cikakken bayani kan manufofinta. Duk da haka shiru-shirunta da halin jajircewa kan komai, sun janyo mata nasara. Hakan ya taimaka mata wajen gudanar da wa'adin mulki hudu.
'Za mu iya'
Kalamanta kalilan sun yi tasiri mai dorewa. Merkel ta samu yabo a sassan duniya kan shirinta na bude kan iyakokin kasashen Turai, don karbar 'yan gudun hijira sama da miliyan guda, masu tserewa daga rikicin Siriya zuwa Turai. Sai dai daidaikun kasashe sun ki yarda da shirin, batu da har ya zuwa yau ya haifar da matsala a siyasar Jamus da Turan.
Lambar yabo a 2015
Mujallar Time Magazine ta karrama Angela Merkel a shekara ta 2015, tare da ayyanata a matsayin "shugabar gwamnatin duniyar walwala da 'yanci." Merkel ta taka rawa a fanonin warware matsaloli dabam-dabam na rayuwa, kama daga tattali da siyasa zuwa zamantakewa.
Mata masu mulki
Da wuya ka ji shugabar gwamnatin Jamus mace ta farko Merkel, ta yi magana kan batun bambancin jinsi. Duk da haka mata sun samu hawa manyan mukamai na tarayya, kamar Annegret Kramp-Karrenbauer (shugabar CDU mai barin gado kuma ministar tsaro),da Ursula von der Leyen (shugabar hukumar gudanarwar Turai) Julia Klöckner (Ministar harkokin noma).
Mai nazari da basirar yanke hukunci
Merkel na da hankali. Takan danne ra'ayinta game da irin shugabannin da kan nuna adawa kusan a kan komai, ta yi mu'amula da su kawai bisa ga muradun gwamnati ko siyasa.
Mai saukin kai da jajircewa
Ta san farashin lita daya na madara, kuma bisa dukkan alamu ko shugabancin kasa na tsawon shekaru bai canja tunaninta ba. Nan a shekara ta 2014 ne, lokacin da ta ziyarci wani shago tare da firimiyan China Li Keqiang. Ba wani sabon abu ba ne ganin Merkel tana yin cefenen gidanta a shagunan birnin Berlin.
Mai rikon amana
An san Merkel da rike hannayen ta wuri daya kamar lu'ulu'u. Ta ce hakan, na taimako wajen saisaita tunaninta. Kuma tabbas ya taimaka wa CDU: Jam'iyyar ta yi amfani da alamar lu'u-lu'u a jikin allunan yakin neman zabenta a 2013. Alamar aminci da kwanciyar hankali.
Rayuwarta, sirrinta
Merkel mutum ce mai matukar sirri. Mutane ba su san komai game da rayuwarta ba, fiye da cewar mijinta Joachim Sauer masanin ilimin lissafi ne. Al'adarsu ce tafiya hutun Ista a tsibiran Ischia da ke kasar Italiya. Sai dai saboda halin da duniya ta ke ciki na annobar corona, ba su samu zuwa hutun Ista na shekarar 2020 ba.
Kwatsam sai ga annobar corona
Ba wai al'adar tafiyar hutun Merkel kawai ba, annobar corona ta sauya muhimman abubuwa da dama a Jamus. Hankalin al'ummar kasar da na sauran kasashe sun juya kanta domin neman mafita daga wannan matsala. Tsarinta na fuskantar matsaloli ka'in da na'in cikin gaskiya, ya janyo mata farin jini da daukaka.
Sai wata rana, uwargida Dr. Merkel
Shekaru biyun da suka gabata ne Merkel ta fito karara ta ce ba za ta sake takara a 2021 ba. Amma za ta cigaba da jagorantar gwamnati kafin lokacin. Tafiyarta a lokacin, na nufin shekaru 16 kenan kan karagar mulki-daidai da wa'adin ubangidanta Helmut Kohl, shugaban gwamnati mafi dadewa a tarihin Jamus.