Mesut Özil ya ce an nuna masa wariya
July 23, 2018Talla
Ulrike Demmer ya ce shugabar gwamnatin tana yabawa da Mesut Özil, saboda irin gudunmowar da ya bayar a fannin kwallon a cikin kungiyar ta Jamus sannan kuma ta ce dole ne a mutunta shawara da ya yanke. Mesut Özil dan shekaru 29 dan asilin Turkiyya wanda aka haifa a Jamus ya ba da sanarwar ficewa daga cikin kungiyar kwallon kafa ta Jamus sakamakon sukar da yake sha daga jaridu bayan hoton da ya yi da shugaban Turkiyya a cikin watan Mayu da ya gabata. Da kuma zargin da ake yi masa cewar shi ne dalilin rashin samun nasara 'yan wasan Jamus a gasar duniya ta kwallon kafa da aka yi a cikin watan Yuni zuwa Yuli a Rasha.