1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mesut Özil ya ce an nuna masa wariya

Abdourahamane Hassane
July 23, 2018

Kakakin Shugabar gwamnatin Jamus Ulrike Demmer ya ce Angela Merkel na muntunta zabin da dan wasan kwallon kafar nan na kasar Mesut Özil ya yi na ficewa daga kungiyar wasannin kwallon kafa ta Jamus.

https://p.dw.com/p/31w16
FC Schalke 04 Mesut Özil
Hoto: Imago/Team 2

Ulrike Demmer ya ce shugabar gwamnatin tana yabawa da Mesut Özil, saboda irin gudunmowar da ya bayar a fannin kwallon a cikin kungiyar ta Jamus sannan kuma ta ce dole ne a mutunta shawara da ya yanke. Mesut Özil  dan shekaru 29 dan asilin  Turkiyya wanda aka haifa a Jamus ya ba da sanarwar ficewa daga cikin kungiyar kwallon kafa ta Jamus sakamakon sukar da yake sha daga jaridu bayan hoton da ya yi da shugaban Turkiyya a cikin watan Mayu da ya gabata. Da kuma zargin da ake yi masa  cewar shi ne dalilin rashin samun nasara 'yan wasan Jamus a gasar duniya ta kwallon kafa da aka yi a cikin watan Yuni zuwa Yuli a Rasha.