1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angela Merkel ta fara ziyarar aiki ta farko a Amirka

January 13, 2006
https://p.dw.com/p/BvCW

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sauka a birnin Washington a ziyarar aikinta ta farko a Amirka tun bayan da ta kama aiki watanni biyu da suka wuce. A yau juma´a aka shirya ganawarta da shugaba GWB a fadar White House. Merkel ta ce zata tabo irin damuwar da Jamus ke nunawa game da kurkukun Amirka da ke a sansanin Guantanamo a can Kuba. Manyan jami´an diplomasiya sun ce Merkel zata kuma yi tayin karin gudummawa da kasar zata bayar wajen sake gina Iraqi, musamman a fannoin ba da ilimi da kuma taimakon jin kai. Kamar tsohuwar gwamnatin Jamus, ita ma sabuwar gwamnatin hadin guiwa ta ce ba zata tura dakarun kasar zuwa Iraqi ba.