Angela Merkel ta gana da fraministan Isra'ila
December 6, 2012Wannan ziyara ta Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a ƙasashen na Turai na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ta ke shan suka daga ƙasashen duniya dangane da shrinta da ta cigaba da yi, na gina matsugunan Yahudawa a gaɓar yamma da kogin Jodan da kuma gabashin birnin Ƙudus.
Jamus wacce ake gani babbar ƙawa ce ga Isra'ila a karon farko ta nuna damuwar ta a kan yunƙurin na kaka gida, wanda ta ce ba aniya ba ce ta ba da haɗin kai ga sake farfaɗo da shirn wanzar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.An shirya shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel za ta tattauna batun na gina matsugunan Yahudawa tare da fraministan Isra'ila, wanda bisa ga dukkan alamu Jamus ɗin za ta baiyana rashin jin daɗinta ga hukumomin Isra'ilan.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal