SiyasaJamus
Angela Merkel ta ja hankalin mata game da siyasa
October 23, 2021Talla
A wata hirar da ta yi da jaridar Sueddeutsche Zeitung, Angela Merkel, ta ce tsarin tafiyar zamanin yau na bukatar mata su rika gogayya da maza a harkar siyasa akasin yanda abin yake a baya.
A cewarta muddin jam'iyyun siyasa na son tafiya da kowa, to lallai ne mata su kasance a matakansu na jagoranci gwargwadon yadda maza ke yi.
Shugabar gwamnati ta Jamus, wadda ta kasance mace ta farko da ta taba rike mukamin shugabancin gwamnati a kasar, ta kawo karshen takararta ne bayan mulkin shekaru 16 a jere.
Armin Laschet, wanda shi ne dan takarar jam'iyyar CDU ta Angela Merkel a zaben da ya gabata, ya bayyana aniyarsa ta jagorantar jam'iyyar kafin lokacin da zai yi adabo da siyasa.
Nan gaba ne dai jam'iyyar za ta sake zaben shugabanninta,