Angela Merkel ta yaba da kudurin kare muhallin da EU ta zartas
March 10, 2007Talla
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana kudurin da KTT ta zartas a jiya game da kare muhalli, da cewa zai zama abin koyi ga sauran kasashen duniya. A cikin sakon ta na bidiyo na mako mako, Merkel ta yi hannunka mai sanda ne ga kasar Amirka da sauran kasashe masu samun matsakaicin ci-gaban masana´antu. Ta ce zata gabatar da kuduri a gaban taron kungiyar G-8 ta kasashe mafiya karfin tattalin arziki hade da Rasha wanda za´a yi a cikin watan yuni a garin Heiligendamm. Ta yi fatan cewa za´a cimma burin da aka sanya a gaba.
“Wannan kuduri da muka cimma wani gagarumin ci-gaba ne a fannin makamashi da yaki da sauyin yanayi tsakanin kasashen Turai. Za´a samu cikakken hadin kai don cimma burin da aka sa a gaba.”