Angela Merkel ta yaba wa matakan tsimi na ƙasar Italiya
January 11, 2012Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta tabbatarwa da Firaministan Italiya Mario Monti cewa ƙasar za ta ci moriyar matakan tsimin da ta ɗauka domin ta da komaɗar tattalin arzikin ƙasar. Shugabannin biyu sun gana yau a birnin Berlin domin gano bakin zaren magance rikicin kuɗin da ya dabaibaye ƙasashe 17 masu amfani da takardun kuɗin euro. Merkel ta baiyana yabo da girmamawa ga Firaministan Italiyan Mario Monti ta na mai cewa ta yi imani ƙasar za ta girbi alheri daga matakan tsimin da ta ɗauka. A nasa ɓangaren Firaminista Monti ya baiyana fatan kasuwannin hada hadar kuɗaɗe za su yi la'akari da irin sadaukarwa da ƙasar ta yi na ɗaukar waɗannan matakai domin samun cigaba mai ma'ana.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita:Zainab Mohammed Abubakar