Bude taron G20 ba Angela Merkel a Ajantina
November 30, 2018Tuni dai Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya isa wajen taron yayin da takwararsa ta Jamus Angela ta samu tsaiko wajen isa saboda tangarda da jirginta ya samu inda ya yi saukar da ba shiri a birnin Kwalan.
Batutuwa da suka shafi tattalin arzikin kasashen na G20 da samar da ababan more rayuwa da batu na zuba jari shi ne abin da ke zama babban kudiri. Sai dai batutuwa da suke daukar hankali a duniya yanzu haka kamar batun rikicin kasuwanci tsakanin China da Amirka da rikicin kasar Ukraine za su ja hankali sosai a yayin taron na Ajantina
Har ila yau a yayin tarukan hadin gwiwa na kasashe da dama da za a yi a kasar ta Ajantina wani batu da ake ganin zai tayar da fushi tsakanin manyan abokai da aka dade ana dasawa, Amirkar da Turai, na zama yadda ake kallon Amirka mai rikon sakainar kashi da batun dan jaridar nan na kasar Saudiyya da aka halaka a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Santanbul na kasar Turkiyya.