Angela Merkel za ta sake yin takara a zaben 2017
November 20, 2016Talla
Wannan dai sanarwa ta kawo karshen rade-radi na cewar ko Merkel da ke zama mace mai karfin fada a ji a duniya za ta sake tsayawa takarar.Duk da sukar da wasu masu zabe a kasar ta Jamus suka yi kan tsarin shugabar gwamnatin na 'yan gudun hijira, ana kallon shugabar gwamnatin a matsayin wata jigo a cikin EU.Kungiyar ta EU ta girgiza dai bayan ficewar Birtaniya daga cikinta yayin da a bangaren guda aka zabi Donald Trump a matsayin shugaban Amirka mai jiran gado.Shugabar gwamnati Angela Merklel dai ta bayyana haka ne bayan tattaunawa da mambobin jam'iyyarta ta CDU a birnin Berlin. Abin da ke share fage na taron jam'iyyar a watan Disamba da ke tafe.