1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rantsar da Shugaba Lourenco na Angola

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 15, 2022

Za a rantsar da Shugaba Joao Lourenco na Angola a wa'adi na biyu a matsayin shugaban kasa, bayan da ya lashe zaben watan Agustan da ya gaba mai cike da takaddama.

https://p.dw.com/p/4Gsmx
Angola | Joao Lourenco | Shugaban Kasa | MPLA
Bayan lashe zabe, Joao Lourenco zai fara wa'adi na biyu na shugabancin AngolaHoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Rahotanni sun nunar da cewa an tsaurarar matakan tsaro a dandalin Praca da Republica mai dimbin tarihi da ke Luanda babban birnin kasar ta Angola, inda za a rantsar da Shugaba Joao Lourenco na jam'iyyar MPLA mai mulki. Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa, an hango jagororin babbar jam'iyar adawa daga nesa. Babbar jam'iyyar adawa a Angolan ta UNITA dai, ta yi korafin cewa an dauki matakin jibge dimbin sojoji a warin rantsar da sabon shugaban ksar ne domin a razana mutane. Ita dai jami'iyyar adawar ta UNITA ta sha kaye ne a hannun jam'iyyar MPLA mai mulki ta Shugaba Lourenco.