1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona na kara yaduwa a Rasha

Gazali Abdou Tasawa
May 5, 2020

A kasar Rasha cutar Coronavirus ta sake hallaka mutane sama da dubu goma a wannan Talata, lamarin da ke zama kwanaki uku kenan ana jere da ake samu mutuwar mutane sama da dubu 10 a kowane yini kasar.

https://p.dw.com/p/3boz3
Russland Moskau | Coronavirus | Test
Hoto: Getty Images/AFP/V. Maximov

Rahotanni daga kasar Rasha na cewa an sake samu a wannan Talata mutane sama da dubu 10 da suka kamu da cutar Covid 19 a cikin yini daya. Kwanaki uku kenan dai a jere da ake samun mutun sama da dubu 10 da suka harbu da kwayoyin cutar a kasar ta Rasha inda kawo yanzu cutar ta harbi a jumulce mutun sama da dubu 155.

 Sai dai kuma annobar ba ta haddasa mace-mace da yawa ba a kasar ta Rasha inda ya zuwa yanzu cutar ta kashe mutun dubu daya da 451 kawai da ke zama adadin mafi karanci idan aka kwatanta da illar da annobar ta yi a kasashe irin su Italiya, Spain da Amirka.

 Sai dai kasashe da dama na nuna shakkunsu kan sahihancin alkalumman matattun da gwamnatin Rasha ke bayyanawa. Alkalumman baya bayan nan dai sun bayyana cewa cutar ta Corona ta harbi mutane miliyan uku da dubu 580 a fadin duniya, daga cikin mutun dubu 252 sun halaka a yayin da wasu miliyan daya da dubu 170 suka warke.