Haïti: Annobar kwalara na daukar rayukan jama'a
October 19, 2022Talla
Mutane 222 sun sake kamuwa da annobar Kwalara da ta barke a baya-bayan nan a kasar Haïti kamar yadda wasu alkaluman hukumomin lafiyar kasar suka zayyana.
Rahoton da ma'aikatar lafiyar kasar ta fitar ya bayyana cewa fursunoni 14 a gidan yarin birnin Port-au-Prince sun mutu, adadin da ya kara alkaluman mamatan ya zuwa yanzu a kasar da ke fama da matsaloli barkatai ciki har da na rashin tsaro.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya nuna matukar damuwa kan halin da kasar ta fada a ciki, yana mai bayyana shi a matsayin mai daukar hankali.