1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta yi gargadin karin yunwa a duniya.

Binta Aliyu Zurmi
May 19, 2022

Babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterress ya yi gargadin cewa yakin da Rasha ke yi a Ukraine ka iya kara barazanar da duniya ke fuskanta na karancin abinci.

https://p.dw.com/p/4BV2Z
Antonio Guterres
Hoto: Loey Felipe/UN Photo/Handout/Xinhua/picture alliance

A jawabinsa da ya gabatar a babban taron koli na Majalisar Dinkin Duniya, babban sakatare na majalisar Antonio Guterress ya yi gargadin cewa duniya na fuskantar karuwar barazanar karancin abinci, kari a kan wanda ta shiga a sabili da sauyin yanayi da ma illar da annobar corona ta janyo.

Mr Guterres ya kara da cewar a yanzu haka yawan mutanen da ke fama da karancin abinci a duniya ya rubanya sau biyu daga miliyan 135 ya zuwa miliyan dari 276 a yan shekarun da corona ta hana ayyukan gona.

Sakataran na MDD ya ce hanya daya mafita ita ce kawo karshen wannan yakin da Rasha ta kaddamar a Ukraine, ya kuma kara da cewa idan aka yi la'akari da irin yawan alkamar da kasar Ukraine ke samar wa duniya da ma yadda Rasha da Belarus ke taka muhimiyar rawa wajen samar da takin zamani da manoma ke matukar bukata, ya kamata masu fada a ji a duniya su dage wajen ganin an kawo karshen yakin baki daya.