1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

APC ta bukaci kotu ta yi watsi da karar Peter Obi

Binta Aliyu Zurmi
April 11, 2023

Jam'iyyar APC a Najeriya ta bukaci kotun daukaka kara da tayi watsi da korafin da dan takarar shugabancin kasar a jam'iyyar Labour Peter Obi ya shigar gabanta na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da ya gabata.

https://p.dw.com/p/4PvAy
Nigeria l APC Ergebnis l Präsidentschaftskandidat
Hoto: Nigeria Prasidential Villa

APC wacce ita ma ta shigar da karar kalubalantar Peter Obi da jam'iyyarsa ta ce a bisa dalilai da dama ya kamata a yi fatali da korafin da suka shigar, daga cikin dalilan APC ta ce a lokacin da jam'iyyar Labour ta mika wa hukumar zabe sunayen 'yan takarar ta, Peter Obi bai sauya sheka ya zuwa jam'iyyar ba, kazalika ta kuma ce bai saka sunan dan takarar PDP Atiku Abubakar a matsayin wanda shi ma ke kalubalantar sakamakon zaben ba.

Peter Obi da ya zo na 3 a zaben da ya gabata, ya ce shi ne ya lashe zaben. Jam'iyyar APC ba ta kai ga cewa uffan a kan karar da Atiku Abubakar wanda ya zo na 2 ba.

Yanzu haka kotun daukaka kara na kokarin samar da alkalai da za su saurari korafe-korafen a kan babban zaben da ma yanke hukunci a kwanki 180 daga lokacin da aka shigar da korafin.