Arangama a Pakistan
August 4, 2007A ƙalla mutane 14 su ka rasa rayuka wasu da dama kuma su ka ji raunuka a sakamakon arangamar da a ka gwanza, tsakanin dakarun gwamnatin Pakistan da yan takifen yankin Waziristan masu tsatsauran ra´ayin addinin Islama.
Wannan yanki da ke arewa maso yammacin Pakistan, ya yi ƙaurin suna wajen nuna ƙyama ga manufofin gwamnati.
Tashe tashen hankulla sun ƙara tsamari, tun bayan murƙushe yan takifen massalacin lal Masadjid na birnin Islamabad a watan da ya gabata.
Wanda su ka rasa rayukan sunhada da sojoji 4 na gwamnati da kuma fara hulla 6, kamar dai yadda kakakin rundunar gwamnatin, Janar Waheed Arshad ya bayyanawa manema labarai.
Ƙasar Amurika da ke matsayin babbar abikiyar ƙawacen shugaba Pervez Musharaf, na zargin sa da nuna sako- sako ga yan takifen Waziristan ,yankin da a cewar fadar mulkin Washington, ya zama tamkar wani sassanni, na mayaƙan Alqa´ida da yan Taliban.