Assad ya gana da babban jami'in Iran
August 7, 2012Shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad ya yi wata tattaunawa ta ba zata a yau dinnan da wani babban jami'in Iran Saeed Jalili kuma babban na hannun daman jagoran addini Ayatollah Ali Khameni yayin da dakarun sojin gwamnatin Siriya ke cigaba da fafata kazamin fada da 'yan tawaye a birnin Aleppo. Iran wadda ta baiyana kakkausar suka game da goyon bayan da kasashen Amirka da Turkiya da Saudiyya da kuma Qatar suke baiwa 'yan tawayen dake yakar Assad ta kuma tura ministanta na harkokin waje zuwa Ankara da kuma wata wasikar da ta aikewa Washington inda ta dora musu alhakin 'yan kasarta 48 wadanda 'yan tawayen Siriya suka yi garkuwa dasu. Saeed Jalili ya kai ziyarar ce bayan ya yada zango a Lebanon kwana guda bayan da Firaministan Siriyan ya sauya sheka. Jalili yace jamhuriyar musulunci ta Iran ta yi imani da tattaunawa a tsakanin dukkan kungiyoyin kasar domin samun sulhu yana mai cewa tsoma bakin kasashen ketare don samun masalaha ba zai amfanar da komai ba. Ya kara da cewa Iran na fatan daukar managarcin matakin cimma wannan masalaha.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Umaru Aliyu