1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Bashar al-Assad ya lashe zaben Siriya da rinjaye

May 28, 2021

Shugaban Kasar Siriya Bashar al-Assad ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Larabar makon nan.

https://p.dw.com/p/3u5eo
Syrien Bashar Al-Assad
Hoto: dpa/picture alliance

Shugaban majalisar dokokin kasar wanda ya sanar da sakamakon zaben ya ce Assad ya samu kaso 95.1 cikin 100 na kuru'un da aka kada. 

A bangaren sauran 'yan takarar shugaban kasar irin su tsohon minista Abdallah Salloum Abdallah ya samu kaso 1.5 a yayin da Mahmud Merhi na gungun 'yan adawar Siriya ya samu kaso 3.3 na kuru'un mutum miliyan 14.2 da hukumar zaben Siriyan ta ce sune suka  yi zaben.

An dai gudanar da zaben a kaso biyu cikin uku na kasar ta Siriya da gwamnati ke da iko, sannan an yi zaben a wasu ofisoshin jakadancin Siriya a wasu kasashen ketare. To amma kasashen Amurka da Burtaniya da Jamus da Faransa da Italiya sun yi zargin cewa an tafka magudi a cikin zaben da ya ba Bashar al-Assad damar yin tazarce a mulkin Siriya. Sai dai shugaban ya musanta wannan zargi.


Wannan dai shi ne karo na biyu da aka zaben shugaban kasa tun bayan da aka fara rikicin Siriya a shekara ta 2011, rikicin da ya lakume rayukan sama da 388,000.