1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Asusun ba da Lamuni ya bukaci sauyi a siyasar tattalin arzikin duniya

Pinado Abdu WabaOctober 10, 2014

Manyan cibiyoyin kudin sun bukaci da a sanya jari sosai wajen ababen more rayuwa da tallafi a nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/1DTFY
Christine Lagarde
Hoto: Reuters/J. Ernst

A taronsu na shekara-shekara Asusun ba da Lamuni na Duniya da Bankin Duniya sun yi kiran da a kara himma wajen zuba jari a kasashe masu tasowa da wadanda tattalin arzikinsu ke habaka a kuma dauki matakai na musamman wajen ganin an kawar da barazanar cutar nan mai hadarin gaske ta Ebola ta yadda duniya ba za ta fiskanci koma baya ba, musamman a fanin tattlin arziki.

Christine Lagard, shugabar Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF ta sami sabuwar kalma, ta kwatanta tattalin arzikin duniya a yanzu haka abin da ta kira new mediocre a turance, abin da ke nufin jinkiri. Da hakan tana nufin tafiyar hawainiyar da ake gani a yanayin bunkasar tattalin arzikin duniya.

A kasashen da suka cigaba, suna cikin damuwa musamman Turai da Japan a yayin da a kasashe masu tasowa kuma Rasha da Brazil sai kuma China da Indiya a yankin Asiya ke taka rawar gani. Matsalar a nan ita ce idan yanayin bunkasar kasashe ba ya bunkasa ya kai yadda ya dace a ce ya kai, lallai za a sami koma ba ya domin zai shafi har bunkasar tattalin arzikin kasashen a shekaru masu zuwa, shi ya sa shugabar ta IMF ta yi kira da a sauya salon siyasar tattalin arzikin domin ta yadda zai bunkasa yadda ya kamata. Ga dai karin bayani daga bakin Christine Lagarde shugabar Asusun Bada Lamuni na duniya.

Ta yaya zuba jari zai taimaka?

A baya dai, Asusun ba da Lamuni na Duniyar ya na dogaro ne da cewa kasuwanci mara shinge, zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki, inda ake batutuwa irinsu kasuwanci mara shinge, bude kasuwanni wa kowani dan kasuwa ya sami damar yin takara da ma mayar da kamfanoni hannun 'yan kasuwa masu zaman kansu. To amma yanzu da yanayin da tattalin arzikin kasashen ya shiga, Asusun tare da Bankin Duniya sun bukaci gwamnatoci da su zuba jari a ababen more rayuwa ta yadda za a samar da bashi ga masu bukata.

Jahrestreffen IMF und World Bank Group in Tokio
Christine Lagarde tare da Jim Yong Kim, shugaban Bankin DuniyaHoto: REUTERS

Shi ma dai shugaban Bankin Duniya Jim Yong Kim na da ra'ayin zuba jari a ababen more rayuwa musamman a kasashe masu tasowa da masu samun cigaba, ya yi kira da a kaddamar da wani shiri, wanda zai zuba jari sosai a tattalin arzikin masu zaman kansu, kuma Bankin Duniyar na kiyasin cewa nan da shekarar ta 2020 za a bukaci kimanin milliyan dubu daya domin rufe gibin da ake da shi a wadannan kasashe na ababen more rayuwar amma a yanzu haka dai abin da ya fiye masa mahimmanci shi ne kawar da cutar Ebola daga kasashen Guinea, Saliyo da Liberiya.