Asusun IMF ya amince da ba Iraki bashin dala miliyan 685
December 24, 2005Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya amince ya ba Iraqi wani bashi na kudi dala miliyan 685. Hakan dai na matsayin wani mataki na taimakawa kokarin da gwamnatin birnin Bagadaza ke yi na farfado da tattalin arzikin kasar. A ci-gaba da tashe tashen hankula a fadin kasar ta Iraqi kuwa an hallaka mutum 12 sannan wasu 25 sun jikata a hare hare biyu da ´yan tawaye suka kai a kusa da birnin Baquba. Sojojin Iraqi 8 sun rasa rayukansu sannan 17 sun samu raunuka a wani harin gurnati da aka kai kan wani wurin binciken ababan hawa dake kan hanyar Bagadaza zuwa Kirkuk. A wani harin kuma an kashe mutum 4 sannan aka jiwa 8 rauni lokacin da wani dan kunar bakin wake ya ta da bam a jikinsa a wajen wani masallacin ´yan shi´a dake garin Baladruz. Hare haren dai su ne mafi muni tun bayan zaben ´yan majalisar dokoki da aka gudanar ranar 15 ga wannan wata na desamba.