Asusun IMF ya nuna damuwa game da hauhawar farashin kayan abinci
April 17, 2011Shugaban Bankin Duniya Robert Zoellick ya nuna kaɗuwa game da tashin gwauron zabi da farashin kayan abinci ke yi a cikin watannin baya bayan nan. A ƙarshen taron farkon shekara da Bankin Duniya da Asusun IMF suka gudanar a birnin Washington Zoellick ya bayyana hauhawar farashin kayan abinci da cewa babbar barazana ce ga ƙasashe matalauta inda ake fuskantar haɗarin rasa wata zuri'a. Alkalumman Bankin Duniya sun nuna cewa farashin ya haura ɗaya bisa uku ida aka kwatanta da bara. Dalilan haka sun haɗa da rashin damina mai albarka, rashin wurare masu kyau na adana abinci sai kuma taɓarɓarewar hanyoyin jigilar kayan abinci. A nata ɓangaren tarayyar Jamus za ta tallafawa ƙoƙarin Bankin Duniya na rage farashin kayan abinci a duniya baki ɗaya, inji ministan ba da taimakon raya ƙasashe masu tasowa na Jamus Dirk Niebel.
"Ya zuwa shekara ta 2012 Jamus za ta kashe Euro miliyan dubu 2.1 wato kwatankwacin dala miliyan dubu 3 a ayyukan raya yankunan karkara."
Bankin Duniya da Asusun IMF na shirin ɗaukar matakai sa ido kan 'yan baranda a kasuwannin kayan albarkatun gona.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar