Asusun IMF zai agaza wa kasar Masar
January 8, 2013Jami'an Asusun bayar da lamuni a duniya na IMF isa birnin Alkahira na kasar Masar domin tattauna yiwuwar tallafawa kasar ta farfado da tattalin arzikinta. Masood Ahmed, darekta a asusun dake kula da sashen yankin Gabas Ta Tsakiya da kuma Asiya, ya ce a wannan Litinin ya gudanar da tattaunawa mai amfanin gaske tare da shugaba Mohammed Mursi na Masar da kuma manyan jami'an gwamnatin kasar akan kalubalen da tattalin arzikin kasar ta Masar ke fuskanta. Ya ce a lokacin tattaunawar ce suka amince da aiwatar da tsare-tsaren inganta sashen bunkasa kananan masana'antu da kuma daukar matakan shawo kan kalubalen tattalin arzikin da kasar ke fama da shi a baya bayannan.
A wani labarin da ya shafi kasar Masar: Akalla yan sanda biyu suka mutu a wani musayar wuta tsakanin jami'an staro da yan bindiga a kudancin kasar. Babban jami'in yan sanda a jihar da lamarin ya faru, yace fada ta barke bayan da yan sanda suka nemi tarwatsa kungun yan fashi da suka addabi yakin. Yan fashin dai sun tsere daga motar yan sanda amma daga bisani an kamo dayansu. Kasar Masar na fama da matsalolin tsaro, tun bayan sauyin gwamnati da aka samu a kasar biyo juyin juya hali da ya kifar da gwamnatin Husni Mubarak.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mouhamadou Awal