1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU da AU sun hada Kai don yakar ta'addanci

Mouhamadou Awal BalarabeApril 8, 2016

Sakatarorin zartsawa na AU da EU sun yanke shawarar tafiya kafada da kafada a lamurun da suka shafi yaki da ayyukan ta'addanci a nahiyoyin Afirka a Turai.

https://p.dw.com/p/1IRk8
Symbolbild Jean-Claude Juncker und Nkosazana Dlamini-Zuma
Hoto: Getty Images/AFP/J. Thys

Kungiyar Gamayyar Turai da takwarata ta tarayyar Afirka za su hada gwiwa wajen yakar ayyukan ta'addanci da ke addabar nahiyoyin nasu guda biyu. Sakataren zartaswa na EU Jean-Claude Juncker da takwrarsa na AU Nkosazana Dlamini-Zuma ne suka cimma wannan matsaya, yayin wani taron hadin gwiwa da suka gudanar a cibiyar AU da ke birnin Addis Ababa na kasar Habasha. A cewarsu shugabannin biyu da,i hada karfi da karfe ne kawai zai iya baiwa Afirka da Turai damar karya kashin bayan masu kaddamar da hare-hare da sunan addini.

Juncker da Dlamini-Zuma sun yi amfani da wannan dama wajen jaddada aniyarsu na yakar 'yan Afirka da ke yunkurin shiga Turai ta barauniyar hanya. Sannan kuma sun tattauna kan rikice-rikice da ke haddasa zubar da jini a kasashe da dama na Afirka, tare da karfafa dangantaka da ke tsakaninsu a fannin yaki da gurgusowar hamada.