1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU za ta dauki sabon salo na yaki da 'yan ta'adda

Abdourahamane Hassane
July 6, 2019

Shugabannin kasashen Afirka na ci gaba da halara a birnin Yamai na Nijar a taron koli na kungiyar tarayyar Afirka wanda zai kaddamar da shirin aiwatar da yarjejeniyar cinikayya mara shinge da kuma yaki da 'yan ta'adda.

https://p.dw.com/p/3Lh5K
Äthiopien Gipfeltreffen der Afrikanischen Union in Addis Abeba
Hoto: Getty Images/AFP/S. Maina

A na sa ran Najeriya wacce da farko ta nuna adawarta da shirin za ta saka hannu kan yarjejeniyar tun a wannan Asabar. Ya zuwa yanzu dai kasashen Eritriya da Benin suka kasance saniyar ware na kin shiga wannan yarjejeniyar cinikayya marsa shinge wacce ta hada mutane miliyan dubu da 200 a cikin kasashe 55 na nahiyar. Sabuwar yarjejeniyar dai na da burin bunkasa huldar cinikayya ta tsakanin kasashen Afirka daga matakin kaso 13 daga cikin dari da take a halin yanzu zuwa kaso 60 daga cikin dari nan zuwa shekara ta 2022. Shugabannin kasashen nahiyar ta Afirka na son soma aiwatar da wannan yarjejeniya daga farkon shekara ta 2020. Bayan batun cinikin shugaban Kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya gargadi sauran shugabannin Afirka da daukar mataki na taron dangi domin yaki da ta'addanci tun kafin lokaci ya kure sakamakon yadda batun ta'addancin ke kara bazuwa a duniya.