1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU ta ce kada a janye sojoji daga Somaliya

Ahmed Salisu
January 27, 2018

AU ta ce janye dakaru da ake shirin yi daga kasar Somaliya a shekarar 2020 bayan wa'adin da aka deba musu ya kare zai taimaka wajen maida hannu agogo baya a kokarin da ake yi na ganin kasar ta samu zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/2re9h
Somalische Friedensmission
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Makaraan

Jami'in da ke shugabantar rundunar wanzar da zaman lafiya a kasar ta Somaliya Francisco Madeira ne ya ambata hakan a wani zama da ya yi wasu shugabannin kasashen Afirka da kuma kasashen da ke bada tallafi wajen wanzar da zaman lafiya a kasar. Madeira ya ce muddin ana son kwalliya ta biya kudin sabulu a aikin da ake yi a kasar ta Somaliya to ya kyautu a kara wa'adin dakarun wanzar da zaman lafiya da ke aiki a kasar. Somaliya ta dau tsawon lokaci ta na fuskantar tada kayar baya daga 'yan kungiyar nan ta Al-Shabaab da ke gwagwarmaya da makamai a kasar kana ta ke kokari wajen girka shari'ar Islama.