SiyasaAfirka
AU ta ja hankalin Habasha da Somaliya
January 4, 2024Talla
Kasar Somaliya dai ta ci alwashin kare yankinta bayan yarjejeniyar wadda ta baiyana a matsayin cin fuska da kuma tsokanar fada kan iyakokinta daga makwabciyarta kasar Habasha.
Karin Bayani: Rikici na ci gaba a yankin Somaliland
Shugaban hukumar tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat a cikin wata sanarwa ya yi kiran nuna halin dattako da mutunta juna tsakanin Habasha da Somaliya.
Ya kuma yi kiran kasashen biyu su fara tattaunawa ba tare da jinkiri ba don warware takaddamar cikin lumana
Faki ya kuma bukaci su kauce wa dukkan wani abu da zai iya kai wa ga bata kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin makwabtan kasashen biyu na gabashin Afirka.