Kungiyar AU na kokarin shawo kan rikicin Burundi
December 18, 2015Talla
Wani wakili a kungiyar ta AU da ya halarci taron da ya tattauan kan batun tura sojojin ya shaidawa manema labarai cewa, kwamitin ya yi amfani da dokar da ta bai wa kungiyar ta AU damar tura dakarun wanzar da zaman lafiyar ba tare da sanar da shugaban kasar ta Burundi ba. An dai gaza samun damar jin ta bakin fadar shugaban kasar ta Burundi da a baya ta yi watsi da batun tura dakarun wanzar da zamn lafiyar. Shugaba Pierre Nkurunziza na Burundin dai na da wa'adin sa'o'i 96 ya bayyana ra'ayinsa dangane da batun tura sojojin na AU, wanda ake sa ran za su rattaba hannu kansa nan da 'yan kwanaki.