1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Australiya ta kama gungun masu laifi

June 8, 2021

Hadin gwiwar 'yan sanda a kasar Australiya sun gudanar da samame da ya basu nasarar kama wasu gungun masu aikata laifi ta manhajar Internet. 

https://p.dw.com/p/3uZDV
 Australien Sydney Scott Morrison PK Operation Ironside Polizei Kriminalität
Hoto: Dean Lewins/AAP via REUTERS

'Yan sandan dai sun kama daruruwan masu laifin ne a kasashe 18 a wani aikin hadin gwiwa na kasa da kasa. Aikin da ya gudana tsakanin Australiyar da kuma hukumar binciken ta kasar Amirka ya sami nasarar bankado masu safarar miyagun kwayoyi a kasar da nahiyar Asiya da Kudancin Amirka da kuma yankin Gabas ta Tsakiya.

Firaministan Australiya Scott Morrison ya ce wannan gagarumin aikin gano masu aikata laifukan ba kasar kawai ya shafa ba, har ma da duniya baki daya.

Kawo yanzu dai Australiyar ta sami nasarar kama mutum 224 tare da kwace makamai masu tarin yawa da kuma tsabar kudi da yawans su ya ka dala miliyan 35, yayin da kasar New Zealand ta ce ta na tsare da mutum 35.